Connect with us

News

Jami’an EFCC Sun Fara Binciken Wasu Mutane 2 Kan Ɓoye Dala $461,600 A Filin Jirgi A Kano

Published

on

Jami’an EFCC sun fara bincike kan wasu mutane biyu, Jamilu Shuaibu Waya da Usman Namadi, bisa zargin ƙin bayyana zunzurutun kuɗin ƙasar waje dala $461,600 a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.

A cewar wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, jami’an shige da fice na shiyyar Kano/Jigawa ne suka kama mutanen biyu ranar Juma’a bayan sun iso daga Dubai cikin jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET941.

Advertisement

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kaddamar Da Sashen Yaki Da Garkuwa Da Mutane A Kano 

Rahotanni sun ce mutanen sun bayyana dala $130,000 da $180,000 ne kawai a wajen tantance kuɗaɗen waje, amma bayan bincike jami’an kwastam sun gano ƙarin dala $120,000 daga hannun mutum na farko wanda hakan ya kai jimillarsa $250,000, yayin da aka gano ƙarin $31,600 daga hannun na biyun wanda ya kai jimillarsa $211,600.

Advertisement

EFCC ta ce kuɗaɗen da ba a bayyana ba sun saɓa da sashi na 3 da 4 na dokar hana safarar kuɗi ta Money Laundering Act 2022. Hukumar ta ƙara da cewa an miƙa waɗanda ake zargin tare da kuɗaɗen da aka ƙwato ga ofishinta na Kano domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da su a kotu.

 

Advertisement

 

Leadership

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending