Connect with us

News

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kaddamar Da Sashen Yaki Da Garkuwa Da Mutane A Kano 

Published

on

FB IMG 1759160530529

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon sashen yaƙi da manyan laifuka irin su fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma ƙwacen motoci.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya ƙaddamar da sashen mai suna Violent Crime Response Unit VCRU a ranar Litinin.

Advertisement

Tankar Mai Ta Kutsa Cikin Gida, Ta Hallaka Kaka Da Jika A Suleja

Ya bayyana cewa an kafa rundunar ce bisa umarnin Sufeto Janar na ’yan sanda, Olatunji Rilwan Disu, da kuma tanadin dokar ’yan sanda ta shekarar 2020.

Advertisement

Ya ce rundunar za ta yi aiki ne bisa tattara bayanan sirri cikin gaggawa tare da haɗin kan al’umma domin magance matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a wasu sassan jihar.

Bakori ya bayyana cewa an zaɓi jami’an rundunar ne bayan horaswa ta musamman kan dabarun yaƙi da manyan laifuka tare da mutunta haƙƙin bil’adama.

Advertisement

Ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa harkokin tsaro, tare da kira ga sarakuna da shugabannin al’umma da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanan masu aikata laifi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending