Connect with us

News

Tankar Mai Ta Kutsa Cikin Gida, Ta Hallaka Kaka Da Jika A Suleja

Published

on

WA 1779097149952

Wata tankar mai ta hallaka wata mata mai suna Maryam Shuaibu da jikanta mai kimanin shekara 10 bayan da ta kutsa cikin gidansu da ke yankin Maje, bayan Garin Suleja a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na safiyar Lahadi, inda rahotanni suka nuna cewa tankar man ta samu matsalar birki kafin direban ya rasa ikon sarrafa motar.

Advertisement

Falalar Kwana Goma Na Farkon Zul-Hijjah: Shawarwari Daga Manyan Malamai

Shaidu sun bayyana cewa direban ya yi yunƙurin ficewa daga cikin motar domin tsira da rayuwarsa, yayin da yaron motar ya karɓi sitiyari domin ƙoƙarin tsayar da ita, sai dai hakan bai yi nasara ba, lamarin da ya sa motar ta kutsa cikin gidan.

Advertisement

Wani mazaunin yankin, Muhammad Badamasi, ya shaida cewa matar da jikanta sun mutu nan take, yayin da wata ƙaramar yarinya ta samu munanan raunuka, inda aka garzaya da ita asibiti domin samun kulawar likitoci.

Hatsarin ya haddasa tashin hankali a yankin, inda matasa suka fito zanga-zanga tare da rufe hanyar Suleja zuwa Minna da kuma hanyar Mahaɗar Dikko da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Advertisement

Wani mazaunin yankin, Abdulmumini Ahmad, ya ce wannan ne karo na huɗu da babbar mota ke afkawa gidan, yana mai danganta lamarin da mummunar lalacewar hanyar da ta ratsa yankin.

Shi ma wani jagoran al’umma, Sani Adamu Numbwa Koro, ya ce sun sha kai koke ga hukumomi kan lalacewar hanyar Maje zuwa Tunga, amma babu wani mataki da aka ɗauka.

Advertisement

“Ba za mu ci gaba da zura ido ana rasa rayukan jama’a saboda lalacewar hanya ba. Muna kira ga gwamnatin jihar da ƙaramar hukuma su gaggauta gyara hanyar kafin aukuwar wani sabon hatsari,” in ji shi.

Rahotanni sun nuna cewa yawaitar tankunan mai a yankin na da alaƙa da kasancewar babban daffon mai na NNPC a Maje, inda direbobi ke yada zango kafin ci gaba da tafiya zuwa Abuja, Kaduna da Minna.

Advertisement

A yayin zanga-zangar, matasan yankin sun koka kan rashin diyya ko tallafin da iyalan waɗanda suka mutu ko suka jikkata ke samu daga hukumomi ko masu motocin da ke haddasa hatsurran.

Lamarin ya jawo cunkoson ababen hawa a Suleja da sauran yankunan da ke makwabtaka da Maje.

Advertisement

Sai dai daga bisani, wata tawaga daga gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Abdullahi Shuaibu Maje, ta samu nasarar shawo kan matasan, inda aka sake buɗe hanyar da misalin ƙarfe 3 na rana.

An binne mamatan biyu a ranar Lahadi bisa tsarin addinin Musulunci.

Advertisement

Babban Kwamandan ’Yan Sanda na yankin Suleja, ACP Muhammad Sani Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Advertisement

 

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending