News
An samu mace-mace a zanga-zangar adawa da tsadar mai a Kenya
Ministan cikin gida na Kenya ya ce mutane hudu sun mutu yayin da fiye da 30 sun jikkata, a tashin hankalin da ya barke a yajin aikin da direbobin safa suka shiga don nuna adawa da hauhawar farashin man fetur.
Minista Kipchumba Murkomen bai fayyace wurare da yanayin da aka kashe ko aka ji wa wadanda abin ya shafa rauni ba, amma “binciken zai tantance ko fararen hula ne marasa laifi ko kuma masu laifi ne suka mutu a lokacin da ake neman kama su,” in ji shi.
Jami’an EFCC Sun Fara Binciken Wasu Mutane 2 Kan Ɓoye Dala $461,600 A Filin Jirgi A Kano
Wannan yajin aiki na fannin sufuri ya haifar da toshe manyan hanyoyi na birane da dama na kasar Kenya, bayan da Nairobi ta kara farashin mai inda dizal ya karu da kashi 45,8% tun bayan fara rikici tsakanin Iran da Amurka. Sai dai masu zanga-zanga sun ta rera kalmar “wantam!” “Wato falle daya ce,” ga wa’adin mulkin shugaban Kenya William Ruto.
Ita kuwa gwamnati ta dora alhakin tashin hankalin kan “‘yan siyasa da ke rura wutar rikici da nufi kai hari kan kadarorin gwamnati da kadarorin magoya bayan gwamnati. A wata hira da ya yi da fara watsa labarai ta NTV, ministan kudi na Kenya John Mbadi ya ce “Wannan yajin aikin ba shi da tushe, duk da cewa farashin mai ya tashi,” yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta kashe ɗaruruwan miliyoyin Euro wajen rage tasirin hauhawar farashin mai a lokacin kasar ke fama da matsin tattalin arziki.
