News
Shari’o’in Zaɓe: Kotu Ta Kawo Sabon Tsari Don Kauce Wa Ƙarewar Wa’adi
Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta ba da umarnin fara karɓar ƙararrakin da suka shafi shari’o’in gabanin zaɓe a ranakun ƙarshen mako da kuma ranakun hutun musamman da gwamnati ke ayyanawa.
Wata sanarwa da Babban Magatakardan Kotun, Yahaya Shafa, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa masu ƙorafi da lauyoyinsu sun samu damar shigar da ƙararraki cikin wa’adin da doka ta tanada.
Sanarwar ta ce za a riƙa buɗe rajistar kotuna daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 2:00 na rana a ranakun Asabar da Lahadi, da kuma ranakun hutun da gwamnati ta ayyana.
Kotun ta ce manufar sabon tsarin ita ce kauce wa duk wani jinkiri da ka iya haifar da ƙarewar wa’adin shigar da ƙara, musamman a shari’o’in da suka shafi zaɓe, waɗanda doka ta ware musu takamaiman lokaci.
Matakin ya shafi shari’o’in da suka danganci zaɓukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa, rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyu da sauran batutuwan da suka shafi shirye-shiryen zaɓukan da ke tafe.
Masu sa ido kan harkokin shari’a na ganin cewa matakin zai taimaka wajen sauƙaƙa wa masu neman adalci da kuma tabbatar da cewa babu wanda zai rasa damar gurfanar da ƙorafinsa saboda ranakun hutu.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
