Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Halaka Ƴan Ta’adda Sama Da 50 A Borno

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji

Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun tsananta ayyuka a arewa maso gabashin Najeriya, wanda ya kai ga halaka ƴan ta’adda fiye da 50, ciki har da wani babban kwamandan ISWAP tare da kame masu taimaka musu da dama a Borno.

Wata sanarwa game da ayyukan dakarun Najeriya da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya samu a yau Laraba, ta ce sojojin sun samu wannan nasara ce bayan ƙaddamar da hare-hare a Borno.

Advertisement

Wani Mutum Ya Rasa Ransa Wajen Dauko Wata Waya Da Ta Fada Rijiya A Kano

 

Advertisement

Rundunar ta ce ta kai hari a yankin Kirta da Arina cika, wanda ya kai ga halaka kwamandojin ƴan ta’adda da dama, ciki har da wani Khalifa Umar, guda cikin gawurtattun mayaƙan ISWAP.

Sanarwar ta ce hare-haren saman da sojin suka ƙaddamar ya tilastawa ƴan ta’addan da suka tsira da rayukansu barin kogonsu da ke cikin tsibiri zuwa kan tudu.

Advertisement

Haka zalika, a wani samame na daban, dakarun Najeriyar sun kame wasu da ake zargin na taimakawa mayaƙan da ababen hawa da kuma bayanan sirri, baya ga wani soja da ya ƙauracewa aiki wanda daga bisani aka gano yana da hannu a muggan laifuka.

Dakarun sun kuma kai hari a yankin Kukawa, inda suka fatattaki ƴan ta’adda tare da gano wasu makamai da suke amfani dasu wajen ƙaddamar da hari a yankunan Borno da kewaye.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending