Connect with us

News

Ƙarancin Ruwa Ya Tilasta Wa Mazauna Wasu Ƙauyukan Kano Shan Ruwan Da Karnuka Ke Wanka A Ciki

Published

on

IMG 20260607 WA0009

Mazauna wasu ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano sun koka kan matsanancin ƙarancin ruwan sha da suke fuskanta, inda suka ce halin ƙuncin ya kai ga wasu iyalai shan ruwa daga tafkuna da ramuka da dabbobi, ciki har da karnuka, ke amfani da su.

‎Mazauna yankunan sun bayyana cewa sun sha kai ƙorafe-ƙorafe ga shugabanninsu a matakai daban-daban, amma har yanzu ba a samu wani sauyi mai ma’ana wajen magance matsalar ba.

Advertisement

An Rufe Shagunan Sayar Da Magani Kusan 600 A Plateau

‎Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Zango, Tudun Fulani, Katsalle, Rimin Na Kuda da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da su a ƙaramar hukumar.

Advertisement

‎Wani mazaunin yankin ya shaida wa Matashiya TV cewa matsalar ta jima tana addabar al’ummomin yankin, inda ya ce sama da shekaru 50 ke nan suna rayuwa cikin ƙuncin rashin ingantaccen ruwan sha.

‎“Mun taso muna ganin wannan matsala, iyayenmu sun same ta, har yanzu ’ya’yanmu suna fama da ita. Wasu lokuta ruwa ɗaya muke amfani da shi tare da dabbobi saboda babu wani zaɓi,” in ji shi.

Advertisement

‎Mazauna yankunan sun ce mata da yara ne suka fi ɗaukar nauyin neman ruwa, inda suke yin tafiya mai nisa domin samo abin amfani na yau da kullum.

‎Haka kuma, wasu yara maza da mata sun bayyana cewa suna yawan rasa zuwa makaranta saboda dogon lokacin da suke ɗauka wajen neman ruwa, lamarin da ke shafar karatunsu da ci gaban iliminsu.

Advertisement

‎Sun yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya janyo ƙaruwar cututtukan da ke da alaƙa da amfani da gurɓataccen ruwa.

‎Mazauna yankunan sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano, Hukumar Samar da Ruwa ta Jihar Kano da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kawo musu ɗauki ta hanyar samar da rijiyoyi da sauran hanyoyin samar da tsaftataccen ruwan sha.

Advertisement

‎Sun ce samar da ruwa ba wai kawai zai rage musu wahala ba ne, har ma zai taimaka wajen inganta lafiya da ilimin yara a yankunan da matsalar ta daɗe tana addaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending