Connect with us

News

ZARGIN KWACE GONAKI: An Kai Sarkin Rano Da Karamar Hukumar Bunkure Kara Kotu

Published

on

kotu

Wasu mazauna yankin Gafan da ke Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano sun shigar da kara a Babbar Kotun Jihar Kano, suna zargin Sarkin Rano da wasu bangarori da yunkurin kwace musu gonaki 27 da suka ce mallakarsu ce ta gado.

Masu karar, karkashin jagorancin Inusa Alasan tare da wasu mutum 26, sun nemi kotun ta hana Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isa, da Karamar Hukumar Bunkure, da kamfanin Syno Hydro Trimming, da Ado Alasan, da wasu mutum tara shiga ko yin wata mu’amala da gonakin da ke yankin Gafan har sai an yanke hukunci a kan shari’ar.

Advertisement

Iran Ta Sanar Da Cewa Ta Kai Hare-hare Kan Manyan Sansanonin Sojin Amurka 18 A Gabas Ta Tsakiya

A takardun karar da aka gabatar wa kotu, masu karar sun ce sun gaji gonakin ne daga iyayensu kuma suna da hujjojin da ke tabbatar da mallakarsu tun shekaru masu yawa.

Advertisement

Tun da farko, a ranar 29 ga Afrilu, 2026, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya bayar da umarnin wucin-gadi da ya hana wadanda ake kara shiga gonakin, noma su, sayar da su, bayar da su haya, jingina su ko gudanar da wata mu’amala a kansu har sai an yanke hukunci kan bukatar da ke gaban kotu.

Kotun ta kuma haramta fara wani gini ko aiwatar da wani sabon tsari a kan filayen da ake takaddama a kansu.

Advertisement

 

Kotun ta dage sauraron karar

Advertisement

A zaman kotun da aka gudanar ranar Laraba, lauyoyin bangarorin biyu sun shaida wa kotu cewa har yanzu ba a kammala isar da takardun karar ga dukkan wadanda abin ya shafa ba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, lauyan masu kara, Abubakar Tijjani Bebeji, ya ce suna neman kotu ta tabbatar musu da hakkin mallakar gonakin tare da bayar da umarnin dindindin da zai hana duk wani yunkurin karbe su.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa umarnin wucin-gadin da kotun ta bayar yana nan daram kuma yana aiki har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar.

A nasa bangaren, lauyan wadanda ake kara, Muhammad Aminu Abdullahi, ya ce wadanda yake wakilta sun mallaki filayen ne bisa ka’ida da doka, yana mai cewa za su gabatar da hujjojin da suka dace a gaban kotu.

Advertisement

Mai Shari’a Nasiru Saminu ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga Yuli, 2026, domin ci gaba da shari’ar bayan kammala isar da takardun da suka dace ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

 

Advertisement

 

Justice Watch News 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending