News
Dakarun Soji Sun Kama Mutane 46 Yan Kasashen Waje Bisa zargin Suna Zaune Tare Da Takardun Izinin Zama Ba
Rundunar Sojojin Najeriya ta ce ta kama wasu ’yan kasashen waje 46 da ake zargin suna zaune a Najeriya ba tare da sahalallun takardun izinin zama ba, a wani samamen tsaro da aka gudanar a wasu sassan jihar Ogun.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka kai jami’an tsaro zuwa yankunan Ijebu Imushin da Ijebu Ilese, inda aka cafke mutanen.
Jam’iyyar NDC Ta Tsayar Dan Kwankwaso A Matsayin Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Zaɓen 2027
Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa wadanda aka kama sun kwashe kusan watanni shida suna zaune a kasar nan ba tare da takardun zama ko wasu takardun shige da fice da suka dace ba.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa daga cikin mutanen 46 da aka kama, mutum 18 ’yan kasar Burkina Faso ne, 23 kuma daga Ivory Coast, hudu daga Togo, yayin da mutum daya ya fito daga Senegal.
Hukumar ta kara da cewa an gudanar da samamen ne a wani bangare na kokarin da jami’an tsaro ke yi na dakile ayyukan da ka iya zama barazana ga tsaron kasa tare da tabbatar da bin dokokin shige da fice.
An mika dukkan wadanda aka kama ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakan da suka dace bisa tanadin doka.
