Connect with us

News

Kotu Ta Yankewa Wani Matashi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Published

on

FB IMG 1781895700804

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wani mutum mai suna Zakaria Garba hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin hannu a harin ta’addanci da aka kai a tashar mota ta Nyanya a shekarar 2014.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa wanda ake tuhumar ya amsa dukkan laifukan da gwamnatin tarayya ta tuhume shi da su, lamarin da ya sa kotun ta same shi da laifi.

Advertisement

Kotu Ta Daure Wata Mata Shekara 10 Kan Safarar Makamai Ga ’Yan Bindiga  A Kano 

Harin na Nyanya, wanda aka kai da bama-bamai, na daga cikin munanan hare-haren ta’addanci da suka girgiza Najeriya. Rahotanni sun nuna cewa fiye da mutum 70 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon fashewar bam din.

Advertisement

Baya ga hukuncin kisa ta rataya da aka yanke masa kan wasu daga cikin tuhume-tuhumen, kotun ta kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai a wani sashe na karar, tare da karin shekaru 35 a gidan yari kan wasu laifuka daban.

Alkalin ya ce hujjoji da bayanan da aka gabatar sun tabbatar da cewa Zakaria Garba ya taka rawa wajen shirya da aiwatar da harin da ya haddasa mutuwar mutane da dama a tashar motar Nyanya.

Advertisement

Kafin ya kammala yanke hukuncin, Mai shari’a Omotosho ya gargadi wanda aka yankewa hukuncin da ya nemi gafarar Ubangiji, yana mai cewa: “Allah Ya ji ƙanka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending