News
Kotunan Majistire Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Kwara

Alƙalan Kotunan Majistire na Jihar Kwara, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Magistrates’ Association of Nigeria (MAN) reshen jihar, sun sanar da cewa za su shiga yajin aiki daga ranar Alhamis, 2 ga Yulin 2026, sakamakon abin da suka bayyana a matsayin rashin ingantaccen yanayin aiki, rashin biyan haƙƙoƙinsu da kuma kulawar da ba ta dace ba daga gwamnatin jihar.
An bayyana hakan ne cikin sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar a ranar Laraba, bayan kammala wani zama da ta gudanar a jihar, inda mambobinta suka nuna matuƙar damuwa da fushinsu kan matsalolin da suka ce sun dade suna fuskanta ba tare da an magance su ba.
Kudirin Kafa Yansandan Jahohi Na Iya Lashe Sama Da Naira Biliyan 800 —Masana
A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar MAN na Jihar Kwara, an ɗauki matakin shiga yajin aikin ne bayan shekaru ana yin watsi da buƙatunsu, musamman waɗanda suka shafi tsarin albashi, biyan alawus da kuma samar da motocin aiki.
Ƙungiyar ta bayyana cewa tsarin albashin da ake biya a halin yanzu ya zama abin takaici da rashin adalci, tana mai cewa alkalin majistire mai matakin albashi na 14 na karɓar albashi ƙasa da wanda magatakardar kotu mai matakin albashi iri ɗaya ke karɓa.
Haka kuma, ta koka kan rashin biyan alawus na sayen kayan ofis, wanda a cewarta doka ta tanadi a riƙa biya duk bayan shekara huɗu. Ta ce ba a sake biyan wannan alawus ba tun daga zamanin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdulfatah Ahmed.
Sauran ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da rashin daidaito wajen biyan alawus na sayen motocin shugabanni, inda ƙungiyar ta ce an bai wa wasu jami’ai wannan haƙƙi, yayin da aka hana wasu ba tare da wani gamsasshen bayani ba.
Ƙungiyar ta buƙaci dukkan mambobinta da su kasance cikin haɗin kai tare da kwantar da hankalinsu yayin da ake shirin fara yajin aikin, tana mai tabbatar da cewa shugabanninta na ci gaba da ƙoƙarin ganin an cimma mafita kan dukkan buƙatun da suka gabatar.
