News
KANO: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jikkata Mutum 12 A Warawa

Ana fargabar cewa aƙalla mutum 12 ne suka jikkata sakamakon wani rikici tsakanin manoma da makiyaya da ya auku a Ƙaramar Hukumar Warawa da ke Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa Lamarin ya faru ne a Gundumar Jigawa inda shafi manoman ƙauyen Gadan Sarki da makiyaya daga ƙauyukan Majawa da Karade, inda rikicin ya samo asali bayan wata saniya ta shiga gonar wani manomi tare da lalata amfanin gonarsa.
Wani mazaunin yankin, Malam Balarabe Ado, ya bayyana cewa manomin ya bugi saniyar ne domin hana ta ci gaba da lalata gonarsa, lamarin da ya fusata mai dabbar, wanda ya rama ta hanyar dukan manomin.
“A nan ne rikicin ya rincaɓe tsakanin ɓangarorin biyu, inda aƙalla mutum 12 suka samu raunuka daban-daban,” in ji shi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Warawa, Alhaji Lamido Sunusi Ahmad, ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Musleem Garindau, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar ya kai ziyara Babban Asibitin Wudil domin duba waɗanda suka jikkata, inda ya bayar da umarnin gwamnati ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen jinyarsu har sai sun murmure.
Ya yabawa shugabannin al’umma da jami’an tsaro kan matakan gaggawar da suka ɗauka wajen dakile rikicin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Hakazalika, ya yi kira ga mazauna yankin da su guji yaɗa jita-jita ko aikata duk wani abu da zai iya ƙara ruruta rikicin, yana mai jaddada muhimmancin tattaunawa da sasanci wajen warware sabani da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
A nasa ɓangaren, kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har zuwa lokacin da aka tuntube shi ba su samu rahoton faruwar rikicin ba, sai dai ya tabbatar da cewa rundunar za ta gudanar da bincike domin tantance abin da ya faru.
