News
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
Akalla gine-gine 200 ne suka lalace bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haɗu da iska mai ƙarfi ya haddasa mummunar barna a birnin Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Lamarin, wanda ya faru da safiyar ranar Asabar, ya shafi gidaje, shaguna, makarantu, wuraren ibada da wasu gine-ginen gwamnati da na masu zaman kansu, tare da jefa mazauna yankunan da abin ya shafa cikin halin ƙaƙanikayi.
Jami’an NDLEA Sun Damƙe Wata Tsohuwa Da Hodar Iblis Kilo 13 Da Aka Ɓoye Cikin Bawon Ayaba
Rahotanni sun nuna cewa ruwan saman ya fara ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe a Ranar Lahadi, inda ya kwashe sama da sa’a guda ana tafka ruwa, lamarin da ya haddasa ambaliya a sassa daban-daban na birnin.
Daga cikin unguwannin da bala’in ya fi shafa akwai Gida Dubu, Takur Site, Mobile, Kudi, Dan Masara, Kwaimawa da wasu yankuna da ke cikin birnin Dutse.
Bincike ya nuna cewa iska mai ƙarfi ta yaye rufin gidaje da shaguna da dama, ta rushe shingaye, sannan ta tumbuke bishiyoyi tare da karya sandunan lantarki, abin da ya haddasa tangarɗa ga samar da wutar lantarki a wasu sassan birnin.
Haka kuma, ambaliyar ruwan ta toshe magudanan ruwa da kwalbatoci, inda wasu mazauna yankin suka danganta matsalar da cunkoson shara da robobi a hanyoyin ruwa, wanda ke hana ruwa gudana yadda ya kamata.
Wasu mazauna sun bayyana cewa rashin share magudanan ruwa kafin fara damina ya taimaka wajen tsananta illar da aka samu, tare da yin gargaɗin cewa ana iya fuskantar ambaliya mai muni idan ba a ɗauki matakan kariya cikin gaggawa ba.
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Jigawa da hukumomin agajin gaggawa da su kai musu ɗauki cikin gaggawa, tare da ɗaukar matakan da za su hana sake aukuwar irin wannan bala’i a yayin da damina ke ci gaba.
-
News4 days ago
Wata Mota Ta Faɗa Cikin Kogin Mayo-Ine A Ngurore
-
News6 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Bada Umarnin Binciken Kuɗaɗen Tsaro Na Ƙananan Hukumomi 44 Cikin Mako Biyu
-
News4 days ago
Ana Zargin Wani Da Kirkirar Hukumar Bogi, Da Nada Kansa Shugaba, Da Karbar Sama Da Naira Biliyan 1 Daga CBN
