Connect with us

News

Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Wani matashi mai suna Ahmad Dankoli ya rasa ransa bayan wasu fusatattun matasa sun lakada masa duka har lahira tare da ƙona gawarsa kan zargin yunkurin satar babur a garin Balare da ke Ƙaramar Hukumar Ajingi a Jihar Kano.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Lahadi, lokacin da ake gudanar da kasuwar mako a garin.

Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Kotun Tafi-da-Gidanka Kan Masu Laifin Miyagun Ƙwayoyi

Ɗan majalisar gundumar Balare, Shu’aibu Abdulmumin Yalo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an zargi marigayin da ƙoƙarin satar babur mallakin wani ɗan kasuwa da ya halarci kasuwar.

A cewarsa, bayan an yi masa wannan zargi, matashin ya yi yunƙurin tserewa, amma wasu daga cikin mutanen da ke wurin suka bi shi, suka kama shi, sannan suka yi masa dukan kawo wuƙa kafin daga bisani su ƙona gawarsa.

Yalo ya ce jami’an tsaro sun isa wurin da lamarin ya faru domin ceto matashin da kuma dawo da doka da oda, sai dai yawan mutanen da suka taru ya hana su shawo kan lamarin.

Advertisement

Ya ƙara da cewa an dade ana fama da sace-sacen babura a kasuwar Balare, lamarin da ake ganin ya haddasa fushin jama’ar da ya kai ga wannan mummunan al’amari.

 

 

DAILY POST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending