News
ICPC Ta Kama Likitan El-rufai Bayan Ganawa Da Shi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta kama likitan tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasiru El-rufai, Farfesa Bello Abubakar.
A cewar ICPC, ta gano wasu hotuna da aka wallafa a shafin Facebook da karfe 2:00 na rana agogon Najeriya, daga hannun dama akwai abokin siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, inda ya bayyana sun kammala ganawa da El-Rufai.
Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Jami’in Gwamnatin China Hukuncin Kisa Kan Badakalar Cin Hanci
Hoton da aka wallafa ya nuna Farfesa Bello Abubakar, Isa Kudan da wasu mutane uku tare da El-Rufai a lokacin da ake zargin yana cikin duba lafiyarsa.
Waɗannan hotuna da saƙon da Isa Kudan ya wallafa sun nuna cewa an yi amfani da damar zuwa asibitin domin wasu ayyuka da ba su cikin abin da kotu da ICPC suka amince da shi.
ICPC ta bayyana hakan a matsayin babban laifi.
