Connect with us

News

Kotu ta Aike da Tsohon Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikta Gidan Gyaran Hali Na Kuje

Published

on

6a4fdb1c7e0a7 (1)

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama da ke birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon shugaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata, Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje.

Mai Shari’a Peter Kekemeke ne ya yi umarnin tsarewar bisa tuhumar da ake yi wa Umar a gaban kotun ta hannun Hukumar Yaƙi Da cin Hanci da Rashawa EFCC, kan zarge-zarge guda huɗu na karya ƙa’idojin aiki lokacin da yana shugabancin Kotun ta CCT.

Na Ƙi Biyan Naira Miliyan 300 Kuɗin Fansa Lokacin da Aka Sace ‘Yan Uwana – Gwamna Dauda Lawal

EFFC ta yi zargin cewa a shekarar 2021 ya yi amfani da asusun bankin matarsa wajen karɓar Naira miliyan biyar daga hannun ɗan kwangila, da aka ɗauko don yin aikin fenti a shalkwatar kotun da ke Abuja.

Ta kuma yi zargin cewa a ranar 25/01/2024 Umar ɗin ya kuma amfani da asusun bankin matarsa, wajen karbar Naira miliyan shida daga wajen wani dan kwangilar da aka bai wa aikin zamanantar da kundin bayanan CCT.

An kuma tuhume shi da umartar wani dan kwangilar da biyan kuɗin makarantar yarsa sama da Naira miliyan biyu a jami’ar Baze da ke Abuja.

Advertisement

Sai dai Danladi Umar dukka ya musanta wadannan zarge-zargen da ake masa.

Bayan yin umarnin tsare shi a gidan gyaran halin, mai shari’a Kekemeke ya ɗage zaman sauraron ƙarar har zuwa ranar 15/07/2026 don sauraron buƙatar neman beli.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending