News
Zaɓen 2027: Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bukaci Dakatar Da Gangamin Siyasa A Kano
Haɗakar wasu ƙungiyoyin fararen hula masu rajin tabbatar da siyasa mai tsafta a Jihar Kano ta buƙaci a dakatar da duk wani gangamin siyasa kafin babban zaɓen shekarar 2027, tare da yin kira ga Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar su gaggauta kafa dokar da za ta hana ƙerawa, mallaka da yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ƙaruwar rikice-rikicen siyasa, ayyukan ‘yan daba da yaɗuwar makamai na ci gaba da zama babbar barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma zaman lafiyar al’umma, tana mai cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, lamarin na iya yin tasiri ga shirye-shiryen zaɓen 2027.
An Sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu Rubuta Jarabawar NECO A Kogi
Da yake jawabi a wani taron manema labarai, Sakataren haɗakar ƙungiyoyin, Auwal Shu’aibu, ya ce yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba na ƙara rura wutar rikice-rikicen siyasa a Kano. Ya yi kira ga gwamnati da ta samar da dokoki masu tsauri da za su hana ƙera, safara da mallakar makamai ba tare da izini ba.
Ya kuma yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban na amfani da ‘yan daba wajen cimma muradunsu na siyasa, inda ya ce ana zargin wasu daga cikinsu da samar musu da makamai. A cewarsa, hakan ne ya haddasa kashe-kashe da tashin hankali a wasu sassan jihar.
Ƙungiyar ta ambaci yankunan Koki, Kasuwar Mayanka (Abattoir), Hotoro, Unguwa Uku, Dorayi Karama da Rimin Kebe da ke bayan ofishin WAEC a matsayin wuraren da aka fuskanci rikice-rikicen da suka yi sanadin rasa rayuka. Haka kuma ta yi nuni da kisan wani jami’in ɗan sanda a Hotoro sakamakon arangama tsakanin ‘yan daba, tana mai cewa matsalar ta shafi jama’a da jami’an tsaro baki ɗaya.
Ta kuma nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin kashe-kashen da ake zargin suna da alaƙa da rikicin siyasa amma ba a gudanar da cikakken bincike a kansu ba, lamarin da ta ce ya haifar da fargaba a tsakanin al’umma tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da zaman lafiya.
Sai dai ƙungiyar ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka wajen ƙarfafa tsaro ƙarƙashin manufar Kano First Agenda, tana mai cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarin matakai masu tsauri domin murƙushe ‘yan daba da kuma hukunta masu ɗaukar nauyinsu.
Daga cikin shawarwarin da ƙungiyar ta gabatar akwai dakatar da gangamin siyasa har sai an tabbatar da ingantaccen tsaro, gudanar da bincike mai zaman kansa kan kashe-kashen da suka shafi siyasa, ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro a wuraren da ake fama da rikice-rikice, samar da ayyukan yi da horas da matasa sana’o’i, da kuma kafa kwamitin zaman lafiya da zai haɗa ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin addinai, na gargajiya da jam’iyyun siyasa domin sa ido da sasanta rikice-rikice.
A matsayin madadin manyan gangamin siyasa, ƙungiyar ta ba da shawarar gudanar da tattaunawa da al’umma, shirye-shiryen rediyo da talabijin, yaƙin neman zaɓe ta kafafen sada zumunta, ziyartar al’umma gida-gida da kuma tarukan unguwanni.
A ƙarshe, ta yi kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su sanya ido kan halin da ake ciki a Kano, tana mai jaddada cewa babu wata manufar siyasa da ta fi darajar rayuwar ko da ɗan Kano guda ɗaya.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
