Connect with us

News

An Kama ’Yan Ƙasar Waje Biyu Kan Zargin Shirya Garkuwa Da Mutum A Kwara

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar da kama wasu ’yan ƙasar Togo biyu da ake zargi da shirya yin garkuwa da wani mazaunin jihar tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 22.

Mai magana da yawun rundunar, SP Adetoun Ejire Adeyemi, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce waɗanda ake zargin sun yi wa mutumin barazanar cewa za su yi garkuwa da shi tare da kashe ƙaninsa idan bai biya kuɗin da suka nema ba.

Kotu Ta Haramtawa Jami’an  FRSC (Road Safety) Tare Motoci A Titunan Kano

A cewarta, bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an rundunar suka gudanar da bincike, lamarin da ya kai ga cafke mutanen biyu tare da ƙwato wata wayar salula da ake zargin an yi amfani da ita wajen yin kiran barazanar.

SP Adeyemi ta ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun amsa suna da hannu a wannan shiri.

Ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da cafke sauran waɗanda ake zargin suna da alaƙa da lamarin, kafin gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Advertisement

 

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending