News
IIIT Ta Horar da Mata ‘Yan Jarida kan Amfani da Kafafen Yaɗa Labarai Wajen Gina Al’umma
DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN
Cibiyar International Institute of Islamic Thought (IIIT) ta shirya taron horaswa ga mambobin Ƙungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen Jihar Kano, domin ƙara musu ilimi kan yadda za su gudanar da aikin jarida cikin gaskiya, riƙon amana da bin ƙa’idojin sana’ar.
A yayin taron, masana sun gabatar da laccoci kan muhimmancin ɗabi’a a aikin jarida, inda suka buƙaci mahalarta da su riƙa amfani da kalamai masu kyau tare da guje wa yaɗa labaran ƙarya, batanci da duk wani rahoto da ka iya haddasa rikici ko fitina a tsakanin al’umma.
Malaman sun bayyana cewa addinin Musulunci ya tanadi kyawawan ƙa’idoji game da yadda ake amfani da harshe da yada bayanai, suna masu jaddada cewa wajibi ne ɗan jarida ya tabbatar da sahihancin labari kafin ya wallafa shi.
Sun kuma ce mata ‘yan jarida na taka muhimmiyar rawa wajen amfani da kafafen yaɗa labarai domin inganta zaman lafiya, haɗin kai da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma. Haka kuma, an tattauna hanyoyin da za a inganta yadda ake gabatar da batutuwan da suka shafi Musulunci cikin hikima da ƙwarewa a kafafen yaɗa labarai.
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar NAWOJ reshen Jihar Kano, Sayyida Bahijja Malam Kabara, ta yaba wa Dakta Bala Muhammad da sauran malaman da suka shirya tare da gabatar da laccocin, tana mai cewa ilimin da aka samu zai taimaka wajen ƙara inganta aikin jarida.
Ta kuma yi kira ga mahalarta taron da su yi aiki da darussan da suka koya, domin tabbatar da aikin jarida mai gaskiya, riƙon amana da kishin ci gaban al’umma.
Daga cikin waɗanda suka gabatar da laccoci akwai Dakta Bala Muhammad, Dakta Sa’idu Ahmad, Dakta Sunusi Uguda, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad, Farfesa Gausu Ahmad, Hajiya Sa’a Ibrahim, tsohuwar Babbar Manajar CTV, Farfesa Aisha Abdullahi Isma’il, da sauran manyan baƙi da suka halarci taron.
