News
Janar Lucky Irabor Mai ritaya ya bukaci A Kama Sheikh Jingir Da Sheikh Gumi Kan Kalaman Tunzura Jama’a
Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace kan wasu malaman addinin Musulunci, ciki har da Sheikh Sani Yahaya Jingir da Sheikh Ahmad Gumi, bisa kalaman da suka yi a baya-bayan nan, wadanda ya ce ka iya tunzura jama’a da kuma kara dagula matsalar tsaron kasar.
Janar Irabor ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda yake mayar da martani kan wasu kalamai da wasu shugabannin siyasa da na addini suka yi kan al’amuran kasar.
Hisbah Za Ta Fara Wani Gagarumin Samame Mai Suna “Operation Kano First “
Tsohon hafsan tsaron ya ce bai kamata hukumomi su yi watsi da kalaman da za su iya haifar da tashin hankali ko kara rura wutar rikici ba, yana mai jaddada bukatar gudanar da cikakken bincike domin tantance manufarsu da illar da ka iya biyo bayansu.
Ya ce idan bincike ya tabbatar da cewa kalaman wani mutum sun saba wa doka ko kuma suna da damar haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin shari’a da ya dace, ciki har da kama wanda ake zargi idan akwai hujjar yin hakan.
Irabor ya kuma jaddada cewa dole ne a rika daukar batun tsaron kasa da muhimmanci, musamman a lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro da dama a sassan Najeriya.
Ya ce ’yancin fadin albarkacin baki ba ya nufin mutum zai yi amfani da kalamansa wajen tunzura jama’a ko kuma kara haddasa rashin zaman lafiya.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
