Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Kwayoyi Da Darajarsu Ta Haura Biliyan 3 

Published

on

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  ta NDLEA sanar da kama wani ɗan kasuwar India ɗauke da muggan ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram dubu 1,550 a jihar Lagos.

Hukumar ta kuma yi nasarar ƙwato ƙwayoyin da darajarsu ta kai naira biliyan 3 da miliyan 600 a jihar ta Legas, baya ga tarin wasu a jihohin Kano da Kwara da Edo da Filato da Oyo da kuma Delta.

El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA Femi Babafemi ya sanyawa hannu kuma ya fitar a yau Lahadi.

Sanarwar ta ce baya ga ƙwace tarin muggan nau’ikan ƙwayoyin, hukumar ta kuma kame tarin masu safarar ƙwayoyin a sassan Najeriya, yayin mabanbantan ayyukan da suka gudanar na baya-bayan nan.

Guda cikin mutanen da NDLEA ta kama sun haɗa da Nwankwo Innocent mai shekaru 48 ɗauke da ƙwayoyi a Legas, sai kuma wani jagoran gungun masu safarar ƙwayoyi da hukumar ta kai samame gidansa, inda ta ƙwace ƙwayoyin da darajarsu ta kai naira miliyan 972,000,000.

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending