Connect with us

News

EFCC Ta Janye Zarge-zargen Da Ta Shigar Akan Maryam Shehu Da Abubakar Shuraim

Published

on

IMG 20260821 WA0014

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin janye zarge-zargen da hukumar ta shigar kan Maryam Isah Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad.

Dabo Fm ta rawaito, an gurfanar da matasan biyu a ranar Alhamis, 20 ga Agusta 2026, a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin aikata laifukan yanar gizo da yada bayanan da hukumar ta ce suna cutar da martabarta.

CS-CRIN Ta Buƙaci ’Yan Jarida Su Jagoranci Yaƙi da Safarar Mutane

EFCC ta ce duk da cewa tana ganin akwai dalilin gurfanar da su bisa tanadin Sashe na 24(2)(c) na Dokar Laifukan Yanar Gizo ta 2015, wadda aka yi wa gyara a 2024, Olukoyede ya yi la’akari da roƙon mahaifin Maryam da kuma kiran wasu ƴan Najeriya na neman a yi musu sassauci.

A dalilin haka, shugaban EFCC ya umarci a janye tuhumar da ake yi wa matasan biyu, tare da gargadin cewa hukumar ba za ta sake lamuntar duk wani hari na ganganci kan martabarta ta kowace hanya ko kafar sadarwa ba.

Olukoyede ya kuma tabbatar wa ƴan Najeriya cewa EFCC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ƙa’ida da kuma abin da doka ta ɗora mata, domin kare muradun ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending