Connect with us

News

FBI Ta Ce Ba Za Ta Iya Sakin Wasu Bayanan Binciken Shugaba Tinubu Ba

Published

on

fbi 750x430

Hukumar binciken laifuka ta Amurka (FBI) ta nemi wata kotun tarayya a Washington DC da ta ba ta damar gabatar da bayanan sirri domin bayyana dalilin da ya sa ta hana fitar da wasu takardun binciken da suka shafi zargin safarar miyagun ƙwayoyi da aka taɓa danganta da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

A takardar da FBI ta shigar a kotu ranar 20 ga Agusta, 2026, hukumar ta ce ba za ta iya bayyana a fili dukkan dalilan da suka sa ta riƙe wasu daga cikin bayanan ba.

FBI Ta Ce Ba Za Ta Iya Sakin Wasu Bayanan Binciken Shugaba Tinubu Ba

Saboda haka, FBI ta nemi izinin gabatar wa alkalin kotun bayanin sirri (ex parte, in camera), wato bayanin da alkalin kaɗai zai duba kuma ba za a saka shi cikin bayanan da jama’a za su iya gani ba.

FBI ta ce sakin wasu daga cikin bayanan na iya fallasa hanyoyi da dabarun binciken jami’an tsaro, tare da yiwuwar jefa rayuka ko lafiyar wasu mutane cikin haɗari.

Bayanan da ake magana a kai sun samo asali ne daga buƙatun neman bayanai guda biyu ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act (FOIA).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending