News
Kwankwaso yace Buhari ya watsawa ‘yan Nigeria kasa a Ido
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gazawa kan harkokin tsaro, ga kuma yaudarar ‘yan Najeriya da gwamnatin ke yi kan cewa suna iya kokarinsu, bayan kuma kullum al’amura lalacewa suke kara yi.
Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Jumma’a, inda yace, zaben 2023 zai shaida juyin juya hali da talakawan Nigeria za su yi na kawar da jam’iyyar APC mai mulki don samar da sabuwar Najeriya.
A gefe guda, Kwankwaso zai bayyana aniyarsa ta neman takarar shugabancin Nigeria cikin sati mai zuwa, a karkashin jam’iyyar NNPP.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
