News
KWANKWASO YA BAYYANA LOKACIN DA ZAI KADDAMAR DATAKARARSA TA SHUGABANCIN KASA.
Daga khadija Abdullahi Mahmud
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirye-shiryen kaddamar da takararsa na shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Daily Nigerian ta rawaito.
Da ya ke magana yayin taron manema labarai a ranar Juma’a, Kwankwaso ya ce “ya tuntubi mutane da dama kuma sun bashi goyon baya”.
“Na tuntubi abokai na yan Najeriya daga bangarori da dama kuma na samu goyon baya. Zan sanar da yan Najeriya takara ta mako mai zuwa,” in ji shi.
News Digest ta rawaito cewa tsohon gwamnan ya nuna gamsuwarsa bisa goyon bayan da NNPP ke samu duba da yadda mutane ke rajista a jam’iyyar.
Ya kara da cewa zaben 2023 za a fafata ne tsakanin wadanda ke son canji da wadanda ke son lamura su cigaba a yadda suke a yanzu.
Kwankwaso ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kara dagewa wurin magance rashin tsaro, yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta karfafa wa hukumomin tsaro gwiwa su kawar da yan ta’adda.
Ya ce a matsayinsa na tsohon ministan tsaro, bai taba tsammanin tsaro zai tabarbare haka ba.
Kwankwason yace ya kamata shugabannin kasar su mayar da hankali wurin horas da sojoji da basu makamai wadanda suka fi na yan ta’addan
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
