Connect with us

News

Aƙalla Mutane 157 Ne Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Zaftarewar Ƙasa Da Ambaliyar Ruwa A Nepal

Published

on

b287443e 6252 4319 8e42 688fd8baec53 1787753342182 (1)

Aƙalla mutane 157 sun mutu, yayin da ɗaruruwan wasu suka ɓace sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa da suka afku a yankunan arewacin Nepal da ke kusa da iyakar ƙasar da Tibet na China.

Bala’in ya afku ne a ranar Laraba, bayan wani zaftarewar ƙasa da duwatsu ya toshe wani kogi, lamarin da ya haifar da gagarumar ambaliyar ruwa wadda ta mamaye gidaje, hanyoyi da sauran ababen more rayuwa.

Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano

Hukumomin Nepal sun ce aƙalla mutane 384 da suka haɗa da matafiya da masu yawon buɗe ido ne aka ruwaito sun ɓace, yayin da ake ci gaba da bincike domin tabbatar da adadin waɗanda suka ɓace da kuma ƙasashensu.

Daga cikin waɗanda aka ruwaito sun ɓace akwai ‘yan ƙasar Nepal da Indiya, Birtaniya, Amurka, Australia, Afirka ta Kudu da Netherlands.

Ministan Harkokin Wajen Nepal, Shishir Khanal, ya ce jami’an tsaro ma na daga cikin waɗanda suka ɓace bayan ambaliyar ta mamaye barikokin su a gundumar Rasuwa.

Advertisement

Ya ce ‘yan sanda 29 da sojojin Nepal 44 ba a san inda suke ba.

Gwamnatin Nepal ta ce ambaliyar ta lalata gadoji da dama, tare da lalata hanyoyi da wasu cibiyoyin samar da wutar lantarki.

Motoci da dama sun kuma tafi da ruwa, yayin da gidaje da wasu gine-ginen gwamnati suka lalace.

Rahotanni sun ce yankunan Rasuwa, Nuwakot da Dhading na daga cikin wuraren da suka fi fuskantar matsalar.

Hukumomin Nepal da China sun ƙaddamar da aikin ceto da neman mutanen da suka ɓace, amma aikin na fuskantar ƙalubale saboda yanayin tsaunuka da lalacewar hanyoyi.

Khanal ya ce wata girgizar ƙasa mai ƙarfin 4.4 da ta afku a yankin na iya kasancewa ta haddasa zaftarewar ƙasa, wadda daga bisani ta toshe kogi tare da janyo ambaliyar.

Advertisement

Sai dai wasu masana na ci gaba da binciken ainihin abin da ya haddasa ambaliyar.

Rahoton Reuters ya ce hotunan tauraron ɗan Adam da binciken farko sun nuna cewa zaftarewar ƙasa mai ɗauke da kankara da duwatsu na iya kasancewa tushen ambaliyar.

A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da aikin ceto, yayin da ake fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu ko suka ɓace zai iya ƙaruwa.

 

 

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending