News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 5 Suna Kokarin Yin Tsafi Da Idanuwan Mutane Da Aka Kwakwale A Bauchi
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da mallakar idanuwan mutum biyu da wasu kayan da ake zargin ana amfani da su wajen tsafin neman kuɗi a Jihar Bauchi.
An kama waɗanda ake zargin ne a wani samame da jami’an Sashen Leƙen Asiri na Shiyya ta 12 na rundunar ’yan sandan Najeriya, da ke Bauchi, suka gudanar.
KANO : ’Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Rogo
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar SP Jalige Mohammad, ya fitar, ya ce jami’an sun kama Abdullahi Idris, Sani Haruna, Auwal Umar, Abubakar Yusuf da Sharu Sale.
Ya ce an ƙwato idanuwan mutum biyu, da tufafi masu launin fari da ja, da kuma wasu kayayyaki da ake zargin ana amfani da su wajen tsafin neman kuɗi daga hannun waɗanda ake zargin.
A cewar sanarwar, yanzu haka ana tsare da waɗanda ake zargin kuma jami’an ’yan sanda na yi musu tambayoyi yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano ƙarin bayanai kan lamarin.
Rundunar ta ce binciken zai kuma taimaka wajen gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, da kuma inda aka samo kayayyakin da aka ƙwato.
Ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu mai hurumin sauraron irin wannan ƙara da zarar an kammala bincike.
Sanarwar ta ce Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da ke kula da shiyyar ya yi Allah wadai da lamarin, tare da kira ga iyaye, masu kula da yara da sauran jama’a da su ƙara sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a da su gaggauta kai rahoton duk wani mutum ko wani aiki da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kawar da masu aikata laifuka a shiyyar da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News3 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
