News
Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, Ya Taya Gwamnan Kano Da Al’umma Bikin Murnar Maulidi Annabi SAW
Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice dake Kano Auwal Lawal Muhammad (Dan Malikin Garo) ya taya gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf da al’ummar jihar Kano da ma Musulmin duniya murnar Maulidin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.
Lawal ya yaba wa gwamnan a kokarin sa na hada kan al’ummar jihar musamman abinda ya shafi addini domin magance rarrabuwar kawuna da fahimtar juna domin kawo zaman lafiya a fadin jihar.
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Sabon Tsarin Samar Da Tsaro, Za Ta Ƙara Tura Makamai Da Motoci Kano
Ya kara da cewar, lokaci ne da al’umma za suyi amfani da shi wajen kara neman kusanci da Allah tare da addu’oin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan ƙasa tamu da kuma jihar mu Kano baki day
Shugaban Asibitin ya kuma yaba kan kokarin da gwamnan keyi na inganta fannin kiwon lafiya, inda ya bada misali da yadda Gwamnan ke gyarawa da inganta asibitoci, samar da kayan aikin likitanci na zamani, da horar da ma’aikatan lafiya.
Daga bisa kwamaret Auwal Lawan ya yaba wa gwamnan bisa sadaukarwa da tsantsar tausayi da yake nunawa, wadanda hakan ke tasiri a rayuwar al’umma.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
