News
Wasu Iyayen Na Da Hannu Wajen Fadan Daba A Wasu Unguwannin Kano – CP Bakori
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce wasu iyaye mata na taimakawa wajen haifar da fadan daba a wasu unguwannin birnin Kano.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan matsalar fadan daba da aka gudanar a yankin Dandinshe, Gobirawa, Tudun Fulani da Silima, da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo.
CP Bakori ya ce iyaye na da babbar rawa wajen dakile matsalar, inda ya bukaci su riƙa tattaunawa da ’ya’yansu tare da sanin irin abubuwan da suke aikatawa kafin matsalar ta kai ga ɗaukar matakin hukuma.
A nata jawabin, mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin tsaro, Ambasada Maimuna Umar Sharif, ta ce haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalar fadan daba.
Ta yi kira ga al’ummar jihar, musamman mazauna unguwanni da kauyuka, da su rungumi irin wannan taro domin bayyana matsalolin tsaro da ke addabar yankunansu da kuma nemo hanyoyin magance su.
A nasa bangaren, ɗaya daga cikin jami’an tsaro, Baba Lili Abdullahi, ya yabawa CP Bakori bisa kokarin da yake yi wajen magance matsalolin tsaro da suka shafi al’ummar jihar.
Ya ce tattaunawa tsakanin jami’an tsaro da al’umma na taimakawa wajen gano musabbabin matsalolin tsaro da kuma samar da hanyoyin da za a magance su cikin lumana.
Haka kuma, Kwamandan Bijilanti, Aminu Usman Kwot, da wasu daga cikin mazauna yankunan da matsalar ta shafa, sun bayyana matsalolin da suke fuskanta tare da bayar da shawarwari kan yadda za a kawo ƙarshen fadan daba.
