Connect with us

News

Yadda Kwararowar Kasuwannni Da Kasuwanci Cikin Unguwa Ke Barazana Ga Unguwar Fagge

Published

on

kasuwa (1)

Daga Salisu Ibrahim Fagge

Al’ummar Unguwar Fagge na kokawa kan yawaitar cunkoson ababen hawa, rashin tsaro da kuma yadda kasuwanci ke mamayar gidaje a cikin unguwa.

Mazauna cikin kwaryar Fagge dake Ƙaramar Hukumar Fagge, a Jihar Kano na ci gaba da nuna damuwa kan yadda cunkoson ababen hawa, matsalar tsaro, rashin kyawawan hanyoyi da kutsen harkokin kasuwanci cikin Unguwar ke zama barazana ga yankin.

 

Fagge, wadda ke daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Kano, na ɗauke da manyan kasuwanni da suka haɗa da Kantin Kwari, Singa da Sabon Gari. Sai dai al’ummar yankin na cewa yawaitar harkokin kasuwanci a wasu manyan tituna da gidaje na haifar da matsaloli ga rayuwarsu ta yau da kullum.

 

Advertisement

A cewar mazauna, wani lokaci daga safe har zuwa dare, wasu daga cikin titunan yankin kan kasance cikin hayaniyar manyan motoci, kaikawon ’yan kasuwa, ga yawan karar injinan samar da wutar lantarki dake saukaka harkokin kasuwanci.

 

Hanyar Ibrahim Taiwo na daga cikin wuraren da ake fama da cunkoso, inda mazauna ke zargin cewa manyan motoci da tireloli masu kai kaya ko sauke kaya a kasuwannin da ke kewaye da yankin kan mamaye sassan hanya.

 

Malam Balarabe Salihi, wani mazaunin hanyar Ikki a Fagge ‘A’ ne, ya ce yanayin ya sa masu amfani da hanyar shiga cikin fargaba, musamman lokacin da suke yara Yan makaranta ke ƙoƙarin tsallaka titi.

 

Advertisement

«“Ba ma sanin daga ina mai tura kurar ruwa zai bullo, sai dai mu yi kacibis da shi, idan da tsautsayi ya ji wa mutum ciwo. Ko ta fustar hanya ɗaya ce, sai mun duba ɓangarorin biyu. Dole mutum ya yi taka-tsantsan, in ba haka ba zai iya ƙarewa a asibiti,” in ji shi.»

 

Kutsawar kasuwanci cikin gidaje

Mazauna yankin sun ce a hankali wasu sassan Fagge da a baya aka fi amfani da su wajen zama sun fara sauyawa zuwa wuraren kasuwanci, shaguna da rumbunan ajiya.

 

Wannan matsalar ta fi bayyana a yankunan da ke kewaye da kasuwannin Kantin Kwari, Singa da Sabon Gari, inda harkokin kasuwanci ke ƙara kutsawa cikin unguwanni.

Advertisement

 

“Matsalar ta fara ne daga shago guda, daga baya suka karu zuwa biyar. Yanzu a hankali, kusan kashi 80 cikin 100 na titin Ibrahim Taiwo ya zama kasuwa,” in ji wani mazaunin yankin.

 

Malam Saleh Ibrahim, ɗan shekara 50 da ke zaune a yankin, ya nuna damuwa kan yadda ayyukan Bureau de Change ke ƙara bayyana a wasu wuraren zama.

 

Ya ce, “Wasu masu sana’ar canjin kuɗi sun shiga cikin wuraren zama, inda aka mayar da wasu gidaje zuwa wuraren kasuwanci.”

Advertisement

 

Mazauna sun kuma yi nuni da hanyar da ta nufi Asibitin Muhammad Jidda General Hospital, inda suka ce ƙananan ’yan kasuwa da sauran harkokin kasuwanci ke ƙara mamaye sassan hanyar.

 

Ƙorafin mazauna kan wakilansu

 

Yayin da mazauna ke bayyana damuwarsu kan sauyin da yankin ke fuskanta, wasu daga cikinsu na tambayar irin matakan da wakilansu da jami’an gwamnati ke ɗauka wajen magance matsalolin.

Advertisement

 

Wasu mazauna sun bayyana damuwa kan matsalolin rashin aikin yi tsakanin matasa, yawaitar yaran da ke yawo a tituna, da kuma yara da ba sa zuwa makaranta.

 

Muhammad Kabir, wani mazaunin yankin, ya ce akwai buƙatar jami’an gwamnati da wakilan al’umma su ƙara sauraron koke-koken mazauna tare da duba hanyoyin magance su.

 

“Da alama wasu daga cikin wakilanmu da jami’an gwamnati ba sa ganin irin matsalolin da al’umma ke fuskanta,” in ji shi.

Advertisement

 

Yayin da ake shiga lokacin shirye-shiryen siyasa da zaɓe, wasu mazauna na cewa ya kamata a fi mayar da hankali kan matsalolin yau da kullum da suka shafi rayuwarsu, maimakon batutuwan siyasa kaɗai.

 

A halin yanzu, Tukur Mohammed, da Muhammad Shehu Bello su ne wakilin mazabar Fagge a Majalisar da na Wakilai, yayin da Yusuf Abdullahi Ata ke riƙe da muƙamin Ministan Jiha mai kula da Gidaje da Raya Birane a gwamnatin tarayya, ga kuma Abudlaziz Abudlaziz, mai bai wa Shugaban Kasa Tinubu shawarma, amma duk da wadannan mukaman na su, ba wani mataki da suka dauka wajen magance matsalolin.

 

Matsaloli biyar da mazauna ke fuskanta

Advertisement

 

Mazauna sun ce matsalolin da ke ƙara damunsu sun haɗa da:

 

Na farko, cunkoson ababen hawa sakamakon manyan motoci, tireloli da ’yan kasuwa da ke mamaye sassan tituna.

 

Na biyu, toshewar magudanan ruwa da tarkacen kasuwanni, wanda suke cewa kan ƙara jefa gidaje cikin haɗarin ambaliyar ruwa a lokacin damina.

Advertisement

 

Na uku, ƙaruwar yawan mutanen da ba mazauna yankin ba da kuma yawaitar harkokin kasuwanci da ake yi har cikin dare, lamarin da wasu mazauna ke danganta shi da ƙarin fargabar satar dukiya da yawaitar yara masu yawon gararanba cikin dare.

 

Na huɗu, akwai yawaitar hayaki da ƙura da manyan motoci ke fitarwa, tare da matsalar zubar da shara, musamman a wuraren da ke kusa da asibiti.

 

Na biyar, sauyin wasu wuraren zama zuwa wuraren kasuwanci, wanda mazauna ke tsoron cewa zai iya rage kyawun tsarin unguwannin tare da ƙara matsin lamba kan abubuwan more rayuwa.

Advertisement

 

Hajiya Aisha, wata uwa da ke zaune a yankin, ta ce: “Gidaje bai kamata su zama shaguna ba, titi kuma ba kasuwa ba ne. Idan aka bar wannan yanayi ya ci gaba, lallai Unguwar Fagge na iya fuskantar matsalar cunkoso.”

 

Ta ƙara da cewa, “A da muna iya tafiyar da alamuran mu har tsawon dare, amma yanzu mutane suna rufe ƙofofin gidajensu tun kafin ƙarfe tara na dare.”

 

Gargadi daga Masana

Advertisement

 

Wani Kwararre wajen tsara birane, TPC Mohammed Habeeb Fagge, ya ce akwai buƙatar hukumomin da abin ya shafa su sa ido sosai kan yadda ake amfani da wuraren zama da na kasuwanci.

 

Ya ce idan gidaje suka ci gaba da rikidewa zuwa shaguna da kuma zama rumbunan ajiya da kuma zama wuraren kasuwanci ba tare da bin ƙa’idojin tsara birane ba, hakan na iya ƙara haifar da cunkoso da matsalolin muhalli.

 

“Birni ba zai samu ingantaccen ci gaba ba idan gidaje suka zama kasuwanni, tituna kuma suka zama wuraren ajiye motoci. Idan hakan ya ci gaba, akwai haɗarin Fagge ta koma wani yanki da za a iya misali da shi wajen matsalar tsarin birane,” in ji shi.

Advertisement

 

Mazauna Fagge yanzu na kira ga hukumomin da abin ya shafa da su duba matsalolin cunkoson ababen hawa, magudanan ruwa, zubar da shara, tsaro da kuma yadda ake amfani da wuraren zama, domin kauce wa ƙara tabarbarewar yanayin yankin.

 

Rahoto: Salisu Ibrahim Fagge

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending