News
Boko Haram, ISWAP Na Ci Gaba Da Barazana Ga Tsaro — Gwamna Fintiri
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na yaƙi da ta’addanci.
Fintiri ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakiyarsa, Farfesa Kaletapwa Farauta, a yayin wani taron shugabannin tsaro da aka gudanar a Yola, babban birnin jihar.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Biyu Bisa Zargin Mallakar Bindigu Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
Gwamnan ya jaddada buƙatar ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, yana mai cewa akwai buƙatar ɗaukar ƙarin matakan tsaro domin dakile ayyukansu da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa tsaron iyakokin ƙasar, tare da samar da na’urorin sa ido na zamani da inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin hana kutsen ’yan ta’adda, dakile hare-hare da kuma hana safarar makamai.
Haka kuma, Fintiri ya yi kira da a ƙara samar wa jami’an tsaro isassun kuɗaɗe da kayan aiki, tare da inganta walwalarsu domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
A wani mataki na ƙarfafa tsaro a jihar, gwamnan ya bayyana cewa an samar da babura 300 da motocin tsaro 16 domin tallafa wa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na Adamawa.
Ya ce samar da waɗannan kayan aikin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na inganta tsaro da ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro domin kare al’ummar jihar daga barazanar ’yan ta’adda.
