News
Jam’iyyar Labour Labour Party Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Hana Jam’iyyun Adawa wuraren sanya Allunan Talla
Jam’iyyar Labour Party a Jihar Kano ta zargi gwamnatin jihar da hana jam’iyyun siyasa samun damar sanya allunan tallan siyasa yadda ya kamata a faɗin jihar gabanin zaɓen shekarar 2027.
Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar na jam’iyyar, Abbas Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da yake nuna damuwa kan yadda Hukumar Kula da Tallace-Tallace ta Jihar Kano (KASA) ke gudanar da tsarin ware wuraren sanya allunan tallan siyasa.
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo
Abbas ya ce hukumar ta nuna shakku kan yiwuwar samar wa jam’iyyar wuraren da suka dace domin sanya allunan tallanta, lamarin da ya ce zai iya kawo cikas ga ƙoƙarin jam’iyyun siyasa na isar da saƙonninsu ga al’umma gabanin zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa Kabiru Saidu Dakata, shi ne shugaban hukumar da aka tuntuba domin neman izinin sanya allunan tallan siyasa, inda ya ce an nuna shakku kan yiwuwar samun wuraren da za a ware wa jam’iyyar.
Ɗan takarar ya jaddada cewa ya zama wajibi a gudanar da dukkan harkokin da suka shafi ware wuraren tallan siyasa cikin gaskiya da bayyana gaskiya, tare da tabbatar da adalci da daidaito ga dukkan jam’iyyun siyasa ba tare da nuna fifiko ga wata jam’iyya ba.
Ya buƙaci hukumar KASA da ta bayyana ƙa’idoji da dokokin da take bi wajen ware wuraren sanya allunan talla a faɗin jihar, domin tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa suna samun dama iri ɗaya.
Abbas ya kuma yi zargin cewa jam’iyyar APC a Kano ta riga ta mamaye mafi yawan wuraren da suka dace domin sanya allunan tallan siyasa, lamarin da ya ce na iya haifar da rashin daidaito tsakanin jam’iyyun siyasa yayin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Ya ce ya kamata a bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar bayyana manufofinsu da shirye-shiryensu ga al’umma cikin ’yanci, bisa tsarin da ya dace da adalci da bin ƙa’idoji.
Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu martanin hukumar KASA da jam’iyyar APC kan zarge-zargen da Labour Party ta gabatar ba.
-
News5 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News4 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News5 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

