Connect with us

News

An Tsige Limami Bisa  Zargin Yi Wa Shuagba Tinubu Kamfen A Masallaci

Published

on

IMG 20261022 WA0029
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

An tsige wani limami a unguwar Madina da ke birnin Bauchi, Dahiru Abubakar, daga mukaminsa bisa zargin amfani da masallaci wajen bayyana goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Rahotanni sun ce limamin ya sha bayyana goyon bayansa ga Tinubu a lokacin wa’azinsa ga masu ibada bayan kammala sallolin farilla.

Ana zargin matakin tsige shi ya biyo bayan kalaman da ya yi bayan sallar Asuba a ranar Lahadi, inda ya ce ba Tinubu ne ya haddasa matsalar rashin tsaro a Najeriya ba, tare da kira da a sake ba shi damar jagorantar ƙasar bayan zaɓen 2027.

Da yake bayyana dalilin kalamansa, Dahiru ya ce yana ƙoƙarin wayar da kan jama’a ne kan cewa bai kamata a ɗora wa Shugaban Ƙasa alhakin dukkan matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta ba.

Ya kuma bayyana cewa matsalar rashin tsaro ba ta shafi Najeriya kaɗai ba, domin ƙasashe irin su Sudan, Chadi da Mali ma suna fuskantar irin wannan ƙalubale.

Sai dai ya ce saƙonninsa sun fi mayar da hankali kan tsoron Allah, kyautata rayuwa da addu’ar samun mafita daga matsalolin ƙasar, duk da cewa yana ƙarfafa jama’a su sake bai wa Tinubu damar jagoranci.

Advertisement

Da yake magana kan matakin, shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce ba goyon bayan Tinubu kaɗai ne ya jawo tsige limamin ba, sai dai zargin mayar da masallacin wajen gudanar da harkokin siyasa.

Jibrin ya ce kwamitin ya sha gargaɗin limamin kan amfani da masallaci wajen tattauna siyasa da tara jama’a domin ayyukan siyasa.

Ya jaddada cewa bai kamata a mayar da masallatai wuraren kamfen ko tarukan siyasa ba, yana mai cewa ofisoshin jam’iyyu da sauran wuraren da suka dace ne ya kamata a gudanar da irin waɗannan ayyuka.

Shugaban kwamitin ya kuma zargi limamin da dagewa kan sauya sunan masallacin daga Masjid Abdullahi Bin Zubbair zuwa Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce kwamitin ya ƙi amincewa da buƙatar, bisa hujjar cewa masallacin mallakin al’umma ne, don haka ba mutum ɗaya ne zai sauya masa suna bisa ra’ayinsa ba.

Jibrin ya ce an yanke shawarar ci gaba da amfani da sunan masallacin na asali, tare da tabbatar da cewa ba za a mayar da Dahiru Abubakar kan mukaminsa na limanci ba.

Advertisement

Ya ƙara da cewa shi da sauran mambobin kwamitin ba sa adawa da Tinubu ko wani ɗan siyasa, sai dai suna son a kiyaye martabar masallaci a matsayin wurin ibada da koyar da addini.

A cewarsa, abin da ya kamata shi ne Musulmi su riƙa addu’ar Allah Ya zaɓa musu shugaba nagari wanda zai kawo alheri ga Najeriya, ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake ciki ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending