Connect with us

News

Tijjani Gandu Ya Maka Gwamnatin Kano Kotu

Published

on

p09yl8m3.jpg
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Fitaccen mawakin siyasa, Tijjani Gandu, ya shigar da ƙara a gaban kotu kan gwamnatin Jihar Kano, bisa zargin yunƙurin tauye masa ’yancin faɗar albarkacin bakinsa.

Mawakin ya ɗauki matakin shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar abin da yake ganin yunƙuri ne na hana shi bayyana ra’ayoyinsa cikin ’yanci, musamman a fagen harkokin siyasa.

Wasu Ƴan bindiga Su Yi Garkuwa Da Makafi Biyu A Filato

Lauyansa, Barrister Aliyu Usman Haji, ne ya bayyana hakan, inda ya yi ƙarin bayani kan matakin shari’ar da Gandu ya ɗauka da kuma dalilan da suka sanya shi garzaya kotu.

Matakin ya biyo bayan takaddamar da ta shafi haƙƙin mawakin na bayyana ra’ayoyinsa, wanda ya ce yana neman a kare masa ta hanyar doka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending