News
Gwamnatin Tarrayya Za Ta Fara Ba ’Yan Kasuwar Jari Bola Lasisi Domin Dakile Satar Kayayyaki

Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin samar da tsarin rajista da bayar da lasisi ga ’yan kasuwar kayan bola domin dakile satar kayayyakin gwamnati da lalata ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.
Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar satar ƙarafa, wayoyin lantarki da sauran kayan more rayuwa, waɗanda masu aikata laifukan ke kwashewa domin sayarwa ga ’yan kasuwar kayan bola.
EFCC Ta Fara Bincike Ciyamomin Ƙananan Hukumomi 774
Gwamnatin ta bayyana cewa wasu daga cikin masu satar kayayyakin kan cire sassan gadoji, hanyoyi da sauran muhimman kayan gwamnati, musamman da daddare, kafin su sayar da su ga masu sana’ar ƙarafa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, da ya sake duba dokokin da suka shafi irin waɗannan laifuka.
A cewarsa, gwamnati na nazarin yiwuwar ƙarfafa dokokin da ake da su domin hukunta waɗanda ke satar kayayyakin gwamnati, da kuma mutanen da ke sayen kayayyakin da aka sace.
Ya ce matakin zai taimaka wajen kare dukiyoyin gwamnati da rage lalata muhimman ababen more rayuwa.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa manufar tsarin ba wai hana halastacciyar sana’ar saye da sayar da kayan bola ba ce, sai dai tabbatar da cewa ana gudanar da ita bisa ƙa’idoji da dokokin ƙasar.
