Connect with us

News

Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Sarkin Lame Kan Zargin Karbar Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba 

Published

on

IMG 20261114 WA0106 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da Sarkin Lame, Yakubu Aliyu, bisa zargin karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba, tsoma baki a harkokin mallakar filaye da kuma ayyukan kamfanonin haƙar ma’adinai.

Mai ba Gwamnan Bauchi shawara kan yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar.

Dalibai Bakwai Sun Mutu Yayin Bikin Murnar Kammala Karatu A Jami’ar Nsukka

Ya ce gwamnatin ta kafa kwamitin bincike mai mutum 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen, inda dakatarwar za ta ci gaba har sai an kammala binciken.

A cewarsa, gwamnati ta samu ƙorafe-ƙorafe da rahotannin tsaro daga shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki kan zargin ayyukan sarkin, waɗanda suka haddasa tashin hankali da fargabar tabarbarewar zaman lafiya.

Gwamnatin ta ce ta gayyaci sarkin domin ya kare kansa, amma bayanin da ya bayar bai gamsar da ita ba, lamarin da ya sa aka kafa kwamitin bincike mai zaman kansa.

Advertisement

Kwamitin wanda tsohon mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda, Sani Mohammed, ke jagoranta, an ba shi makonni uku domin miƙa rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnati.

Sai dai gwamnatin ta jaddada cewa zarge-zargen ba su zama hujjar laifi ba tukuna, kuma za a ba sarkin damar kare kansa bisa ƙa’idojin adalci.

A yayin dakatarwar, gwamnatin ta umarci sarkin da ya kasance a cikin masarautarsa, tare da hana shi tsoma baki a harkokin gudanarwar masarautar.

Haka kuma, an umarci wani babban kansila a masarautar, Bala Abubakar, da ya riƙa kula da ayyukan yau da kullum na masarautar har zuwa lokacin kammala binciken.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending