Connect with us

Politics

Babu inda nace zan kawo karshen tasirin Kwankwaso da Shekarau a siyasa — A A Zaura

Published

on

AA Zaura

Daga yasir sani Abdullah 

 

Advertisement

 

Dan takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim (A A Zaura), yace an jawo hankalinsa kan wasu wallafe wallafe dake zagayawa yanzu haka a jaridun yanar gizo gizo, inda ake ikirarin yace, “zai kawo karshen tasirin siyasar Kwankwaso da Shekarau a Kano” inda yace bai fadi haka ba, hasalima ya kirasu da iyayensa a cikin hirar da ake dakko zancen.

Advertisement

Abinda nace a lokacinda Yan Jaridu suka tambayeni: “Yaya Kake ganin Fuskantar manyan jiga jigai guda 2, tsofaffin Gwamnoni, sanatoci Kuma tsoffin ministoci a wannan zabe na shekarar 2023?

Abinda nace shine, ” da yaddar Allah, ni zan Lashe zaben 2023, idan Allah ya bani, kaga sai Malam ibrahim Shekarau da Sanata Rabi’u Musa kwankwaso suje su huta, dukansu sunyi aiki tukuru a lokutansu, Kuma idan ka duba, zakaga sadda sukayi wannan kokarin sunada jini a jika, saboda haka wadannan iyayen nawa guda biyu zasuje su huta insha ALLAH a shekarar 2023″

Advertisement

“Inaso Al’umma su sani cewa ban taba aibanta ko cin zarafin Koda sa’a naba, balle wanda nake Kallo a sa’oin iyayena Kuma nake kallonsu a iyaye. Ban taba daukar Siyasa a Batanci ba, Kuma ban yadda da Siyasar cin zarafi, Mutunci da Batanci ba. Muna Siyasa Kuma ta muntuntawa da Karramawa don cigaba.

“Ina kira ga gidajen jaridun da suke yada wannan irin labaran kanzon kurege da suguji ayi amfani dasu don cimma burin Siyasa ganin cewa Hakan nada illa hatta a Shari’ance

Advertisement

Nagode.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending