Connect with us

News

Gwamnatin Buhari ce Gwamnatin da ta fi kowacce cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya_Bishop Oyedepo.

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Shugaban Cocin Living Faith ta Najeriya, Bishop Oyedepo ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin da ta fi kowacce gwamnati shuhura wajan cin hanci da rashawa, tunda daga sanda aka kafa ƙasar.

Yan bindiga sun sace limamin coci da matarsa a Kwara

 

A jawabinsa na wani taro da aka gudanar a cocin tasa, Bishop ɗin ya alaƙanta halin matsi da wahalar rayuwa da masu ƙaramin ƙarfi suke ciki da yawaitar cin hanci da rashawa a wannan gwamnatin ta shugaba Buhari.

Advertisement

 

Oyedepo ɗin ya kara da cewa, ƙuɗaɗen da ake zargi tsohon babban akanta na ƙasa ya handame sun isa ace sun warware matsalar yajin aikin da jami’o’in ƙasar nan suka shafe sama da wata 4 suna yi.

 

A ƙarshe Bishop Oyedepo yace babu wani yaƙi da cin hanci da rashawa da wannan gwamnatin take yi.

 

Idan za’a iya tunawa, a cikin watan Mayun da ya gabata ne gwamnatin Buharin ta dakatar da babban akanta na ƙasa Ahmed Idris bisa zargin da almindahanar kuɗi wanda yawan su ya kai kimanin biliyan 80. Sannan kuma ta maye gurbinsa da Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku wanda shi ne yake da tarin laifuffukan alhmundahana da ake tuhumarsa da su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending