Connect with us

News

An nada sabon Sarkin Kwatarkwashi

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud 

 

 

 

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta sanar da nadin Alhaji Garba Ahmad Bunu a matsayin sabon Sarkin Kwatarkwashi.

PDP ta kafa kwamitin nemo wa Atiku mataimaki

Advertisement

 

Sanarwar nadin da aka fitar ranar Talata na dauke ne da sa hannun Sakataren Gwamnatin jihar ta Zamfara Kabiru Balarabe Sardauna.

 

Sabon Sarkin da ne ga marigayi Alhaji Ahmad Umar, wanda ya rasu makon da ya gabata.

 

Marigayi Alhaji Ahmad Umar ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya, yana da shekaru 93.

Advertisement

 

Ya hau mulki ne tun a ranar 17 ga watan Maris din 1961, shekaru 61 ke nan yana mulki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending