News
Shugaba Buhari nayi duk mai yiwuwa wajen magance matsalar karancin gidaje ga yan Najeriya – FHA MD
Daga yasir sani abdullahi
Hukumar samar da gidaje ta kasa ta ce shugaban kasa Muhammad Buhari yanzu haka nayi duk mai yiwuwa wajen magance karan gidaje ga yan Najeriya.
Babban daraktan hukumar Sanata Gbenga Ashafa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya kara da cewa kafin karewar wa’adin mulkin Buhari matsalar zata zama tarihi, domin kuwa kowa zai dara kan ci gaban da za a samu a bangaren.
Yayin da yake jawabi a wajen wani taron wayar da kai da aka shirya a rukunin gidajen na Lugbe, ya ce yanzu haka akwai shirye shirye da dama da aka bujiro da su, da nufin ganin an samu waraka ga matsalar.
Ya kuma ce yanzu haka akwai gidaje 300 da tuni aka kammala su a yankin Zuba, dake Abuja.
A cewar sa, gidajen an samar da su ne domin tallafawa masu kananan karfi su samu damar mallakar gidajen cikin sauki.
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News3 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
