Connect with us

News

Yarima Bin Salman ya kai ziyara Turkiyya tun bayan kisan Khashoggi

Published

on

Daga kabiru Basiru Fulatan

 

 

 

 

Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman na kan hanyar zuwa Turkiya, ziyararsa ta farko tun bayan kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi a wani ƙaramin ofishin jekadancin Saudiyya da ke Santanbul.

Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar siyawa Alkalai mota

Advertisement

Kisan ɗan jaridar wanda ya fusata ƙasashen duniya shekaru huɗu da suka gabata, ya mayar da Saudiyya saniyar ware ta fuskar diflomasiyya.

Yanzu shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai yi maraba da Yariman na Saudiyya wanda ya musanta zargin a kisan Mista Khashoggi.

Masharhanta na ganin sabon tsarin Saudiyya na zuba jari zai taimaka wa Turkiyya haɓaka tattalin arzikinta da ke cikin matsala.

Mohammed bin Salman ya ziyarci Jordan da birnin Alkahira na Masar a farkon wannan makon kafin balaguron nasa zuwa Turkiyya.

Sources BBC Hausa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending