News
Ba Ni Da Wani Burin Yin Tazarce, Domin Wanda Ya Gwada Yin Hakan Bai Kwashe Lafiya Ba -Buhari Ga Boris Johnson
Daga Yasir sani abdullahi
Ya yi magana ne a taron kasashen biyu tare da Firamistan Burtaniya, Boris Johnson
A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai sake tsayawa takara karo na uku ba.
Gasar Firimiya ta Ƙasa: Ciyaman ɗin Pillars ya naushi mataimakin alƙalin wasa a Kano
Ya yi magana ne a taron kasashen biyu tare da Firamistan Burtaniya, Boris Johnson.
An gudanar da taron ne a gefen taron shugabannin kasashen renon ingila wato Commonwealth karo na 26 a birnin Kigali na kasar Rwanda.
Buhari ya nanata kudurinsa na mutunta iyakar wa’adin mulkinsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Firaministan ya nemi ko shugaban Najeriya zai sake tsayawa takara.
“Wani lokaci kuma? A’a! Mutum na farko da ya gwada hakan bai kare lafiya ba,” in ji shi.
Dangane da rashin tsaro kuwa, Buhari ya ce bayan gwamnatin Muammar Gadaffi, jami’an dauke da makamai a kasashen yankin Sahel na tada tarzoma.
“Abin da kawai suka san yadda ake yi shi ne harbin bindigogi”, in ji shi.
