Connect with us

News

Sheikh Gumi Ya Gargadi Jami’an Tsaro Kan Kama Matasan Fulani Barkatai Da Sunan Yaki Da Yan Bindiga.

Published

on

Daga Yasir sani abdullahi

 

Advertisement

 

Fittacen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi hukumomin tsaro game da kama matasan fulani barkatai da suna yaki da ta’addanci.

Advertisement

Ba Ni Da Wani Burin Yin Tazarce, Domin Wanda Ya Gwada Yin Hakan Bai Kwashe Lafiya Ba -Buhari Ga Boris Johnson

Da ya ke magana da wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya a Kaduna, Sheikh din ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa a wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare.

Advertisement

Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar nan.

Yace “Kwanaki kadan da suka gabata, wani mutum ya kira ni ya ce jami’an tsaro sun kama yara bakwai da ba su aikata laifi ba a ranar 17 ga watan Mayun 2022 kuma tun ranar babu labarinsu. Akwai kuma labaran batar matasan Fulani da yara ba tare an sake ganinsu ba.”

Advertisement

Akwai wadanda ake tsare wa ko a tura gidan yari na shekaru babu shari’a. Idan wani ya aikata laifi, doka ya ce a kai shi kotu cikin awa 24 amma ana ajiye matasan nan tsawon shekaru babu shari’a, wasu sun mutu a tsare.

Bai kamata wannan na faruwa a kasar nan ba. “An kafa kungiyar Nomadic Right Concern Group ne don nema wa yaran da aka kama ba tare da laifi ba adalci.

Advertisement

Wadanda aka samu da laifi a hukunta su yadda doka ya tanada amma wadanda ba su da laifi a sake su saboda adalci da daidaito. Dole a dena kama matasa da yara barkatai,” in ji shi.

Ya yi bayanin cewa cikin ayyukan kungiyar, akwai gano adadin yaran Fulani wadanda aka tsare da su kuma ba su da laifi da neman lauyoyi da za su fitar da su.

Advertisement

Da ya ke magana kan kafa kungiyar, Shugabanta Farfesa Umar Labdo, ya ce kungiyar ba ta Fulani ne kadai ba, amma dukkan makiyaya, daga kowanne kabila, yanki da addini.

Ya ce kungiyar za ta zama murya ga makiyaya da ba su da karfin fada a ji inda za su iya yi wa kasa bayanin matsalolinsu da bukatunsu da abin da suka fatan cimma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending