Connect with us

News

Da Ɗuminsa: Kotun Ƙoli Zata yanke hukunci kan sashe 84 (12) na Dokar Zaɓe a yau

Published

on

Daga Yasir sani abdullahi

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A yau Juma’a ake saran jin hukunci na ƙarshe kan inganci da sahihancin sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Zaɓe da Kotun Ƙoli ta Najeriya zata yanke hukunci.

Advertisement

 

Kotun Ƙarshen zata yanke hukunci ne akan Majalisun Ƙasa da Antoni-Janar na Kasa kuma Ministan Shari’a.

Advertisement

 

 

Advertisement

Wakilin Majiyar mu ya samu bayanan cewa za’a yanke hukuncin a yau, inda Kotun zata faɗi matsayar ta a wannan safiyar.

Sheikh Gumi Ya Gargadi Jami’an Tsaro Kan Kama Matasan Fulani Barkatai Da Sunan Yaki Da Yan Bindiga.

Advertisement

An bukaci Shugaba Buhari da Majalisun Ƙasa dasu hallara a Kotun domin yanke hukuncin.

 

Advertisement

 

Shugaba Buhari da Abubakar Malami sun shigar da ƙara a Kotun Ƙoli inda suka buƙaci a basu hukunci akan sashen Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022.

Advertisement

 

A cikin ƙarar da aka shigar a ranar 29 ga watan Afrilu, Shugaba Buhari da Malami wanda suka shigar da ƙarar, sun lissafo Majalisun Ƙasa a matsayin wanda ake ƙara.

Advertisement

 

Sashe na 84 (12) ya haddasa ruɗani da muhawara a Najeriya, tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa Dokar hannu da aka yiwa gyaran fuska a watan Fabrairu na wannan Shekarar.

Advertisement

 

Jim kaɗan bayan ya sanya hannu ga Dokar, Shugaba Buhari ya buƙaci Majalisa data goge sashen, inda suka ƙi yin abinda ya buƙata.

Advertisement

 

A cewar Dokar ta sashe na 84 (12) babu wani mai muƙamin siyasa a kowani mataki da zai yi zaɓe a matsayin Deliget, ko a zaɓe shi, inda don yayi takarar zaɓe ne.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending