News
Karin ‘yan Najeriya miliyan 10.4 sun yi rajistar zabe, in ji INEC
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Sama da mutum miliyan 10 ne suka yi rajistar zabe a aikin rajistar da ake ci gaba da yi a yanzu a fadin Najeriya.
Hukumar zaben kasar, INEC ce ta bayyana haka a ranar Litinin.
Alkaluman bayanan sun nuna cewa sabbin masu rajistar sun kai 10,487,972, wadanda kuma suka kammala yin rajistar gaba daya sun kai 8,631,696.
Ya zuwa karfe bakwai na safiyar jiya Litinin 27 ga watan Yuni 2022, masu yin rajistar ta intanet sun kai 3,250,449, masu zuwa da kansu domin a yi musu rajistar kuwa, 5,381,247 ne.
Bayanin ya kuma nuna cewa daga cikin sabbin masu neman rajistar 4,292,690 maza ne yayin da 4,339,006 mata ne, masu nakasa kuma 67,171 sai matasa 6,081,456.
Hukumar zaben ta ce kara lokacin yin rijistar abu ne da ya zama wajibi a gareta ganin irin yadda mutane suka yunkuro da sha’awar mallakar rijistar da kuma yadda ‘yan kasar ke neman a kara lokacin, wanda a da ta sanya ranar 30 ga watan nan na Yuni ta zama rana ta karshe ta aikin.
