News
2023: Karanta Jihohin da masana sukace Atiku da Tinubu zasu lashe zabe a cikinsu
Dagac kabiru basiru fulatan
A yayin da zaben shemarar 2023 ke kara matsowa, masana na ta bayyana ra’ayoyi Kan yanda zaben zai iya kasancewa.
A yayin da Bola Tinubu ya fito daga bangaren jihohin Yarbawa da suka hada da Lagos, Ondo, Ogun, Osun, Oyo da Ekiti, ana sa ran babu wanda zai kai masa wargi a wadannan jihohi, shine zai lashesu.
Rundunar Soji Sun Yi Watsi Da Rahoto Kan Rashin Kayan aiki, Da Jin Dadin Jami’ai
A yankin Inyamurai da kudu maso kudu kuwa, Atiku da Tinubu duk basu da karfi sosai, saidai Ana tunanin tunda APC na rike da jihohin Imo, Ebonyi, da Cross River, Tinubu zai iya samun wani abu a wajan.
Wasu gwamnonin Arewa ma zasu iya baiwa Tinubu hadin kai ko da bai ci ba, ya samu kaso 25 da ake bukata daga jihohinsu.
A bangaren Atiku kuwa, yana da gagarumar barazana inda a Arewa, babbar jihar Kano, Kwankwaso ya fito takara, a jiharsa ta Adamawa ma da ake tunanin zai kai Labari, tuni wasu manyan jihar irin su Nuhu Ribado sun nuna karara suna tare da Tinubu ne, wanda hakan ke nuna za’a yi jani in jaka wajan lashe zaben jihar tsakanin Tinubu da Atiku.
A jihohin Arewa maso yamma ana tunanin Atiku zai taka rawar gani sosai musamman saboda wadannan jihohin da wuya su zabi wanda ba dan Arewa ba.
A jihohin Arewa ta tsakiya kuwa watakila a yi raba daidai tsakanin Tinubu da Atiku.
