Connect with us

News

Muna daukar matakin rarrashin wadanda suka fusata a PDP – Atiku

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya ce suna daukar matakin wajen yin sulhu da mutanen da aka batawa a jam’iyyar.

A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yana kaunar kowanne dan jam’iyyar, cikinsu har da gwamnoni.

View more on twitter

“Peoples Democratic Party (PDP) za ta ci gaba da kasance a dunkule. Ku mayar da hankali kan matakan da muke dauka. Muna daukar matakai domin shawo kan korafin kowa,” a cewarsa.

Advertisement

“Hadin kan jam’iyyarmu shi ne babban abin da na sanya a gaba. Matakin farko na hadin kan Najeriya zai soma ne daga jam’iyyarmu zuwa cikin al’umma,” in ji Atiku Abubakar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending