News
Muhammad Abacha muka sani a dan takarar gwamnan Kano na PDP — INEC
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta sanya ido kan zaben fidda gwani na dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP a bangaren Shehu Wada Sagagi ne, ba wani bangare daban ba.
Ukraine: Najeriya Ta Shirya Wadata Kasashen Turai Da Man Gas—– Buhari
Kwamishinan zabe na hukumar INEC a jihar Kano, Riskuwa Arabu Shehu, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, a lokacin zaben fidda gwani, shari’a ta amince da tsagin da Sagagi ke jagoranta.
Riskuwa ya bayyana cewa, wasikar da shugaban jam’iyyar PDP ya aike wa hukumar ta bayyana sunayen wadanda suka sanya idanu a zaben daga shalkwatar jam’iyyar PDP ne kawai.
Sai dai ya jaddada cewa doka ba ta tilasta INEC ta amince da duk wani suna da jam’iyya ta gabatar daga zaben da ba ta sanya ido akai ba.
