News Sojoji Sun Sake Ceto Karin Wata ‘Yar Makarantar Chibok Da Aka Sace Published 4 years ago on July 1, 2022 By KABIRU BASIRU FULATAN Share Tweet Facebook Twitter Pinterest LinkedIn WhatsApp Copy Link Daga Khadija Abdullahi Mahmud Advertisement Sojojin Najeriya sun ceto karin wata dalibar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus da aka yi garkuwa da ita tare da wasu da dama daga makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati dake Chibok a Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilun shekarar 2014.Advertisement FAUSTIN-ARCHANGE TOUADERA NA SHIRIN YUWA HUNDIN TSARIN MULKI GYARAN FUSKA Wani rahoton sirri da Zagazola Makama, masani a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ya samu daga manyan majiyoyin soji, wanda wakilinmu ya samu, ya nuna cewa Sojojin Birged 21 masu sulke ne suka ceto Ruth da danta a Bama ta jihar Borno a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022, bayan ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram a yankin karamar hukumar Bama ta jihar.Advertisement A yayin da take ba da labarin irin halin da ta shiga, Ruth ta ce ta tsere daga dajin Sambisa shekaru takwas bayan da ‘yan ta’addar Boko Haram suka sace ta daga makarantarta da ke garin Chibok. Ta ce bam ne ya kashe mijin ta ‘dan ta’adda a lokacin da yake kokarin tayar da shi a kan dakarun Operation Hadin Kai da ke yankin Arewa maso Gabas.Advertisement Ruth ta kara da cewa har yanzu sauran ‘yan matan makarantar na tare da wadanda suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa. “Na dauki kwanaki uku ina tserewa daga yankin ‘yan tada kayar bayan. Na dauki abinci tare da ni don yarona. Wasu daga cikin ‘yan Boko Haram sun ganni a lokacin da nake fitowa amma sai na gudu daji don gudun kada su sake kama ni,” inji ta.Idan dai za a iya tunawa a makonni biyu da suka gabata ne Sojojin suka kubutar da ‘yan matan makarantar Chibok guda biyu, Mary Dauda da Hauwa Joseph, bayan sun tsere daga sansanin Gazuwa, hedikwatar kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād da aka fi sani da ita.Advertisement Kubucewar nasu ya biyo bayan gagarumin farmakin da dakarun Operation Hadin Kai suka ci gaba da kaiwa, wanda ya janyo yunwa da kaura a yankunan ‘yan ta’addan. Har indaranka ta rawaito cewa Boko Haram ta yi a won gaba da dalibai mata 276, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2014. Sama da 100 daga cikin ‘yan matan makarantar ne har yanzu ba a san inda suke ba tsawon shekaru takwas bayan da ‘yan ta’adda suka sace su.Advertisement Facebook Twitter Pinterest LinkedIn WhatsApp Copy LinkAdvertisements Related Topics:Sojoji Sun Sake Ceto Karin Wata ‘Yar Makarantar Chibok Da Aka Sace Up Next Kungiyar Kwadago Ta Kira Zanga-Zanga Kan Yajin Aikin ASUU Don't Miss FAUSTIN-ARCHANGE TOUADERA NA SHIRIN YUWA HUNDIN TSARIN MULKI GYARAN FUSKA Advertisement You may like Click to comment Leave a Reply Cancel replyYour email address will not be published. Required fields are marked *Comment * Name * Email * Website Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment. Latest Popular Videos News1 day ago Sare Bishiyoyi A ARTV Ya Bankado Matsalolin Da Ke Addabar Tashar — Gwamnatin Kano News2 days ago Kazafin Satar Mace Ya Janyo Wa Dan Acaba Duka News2 days ago Ƙarancin Ruwa Ya Tilasta Wa Mazauna Wasu Ƙauyukan Kano Shan Ruwan Da Karnuka Ke Wanka A Ciki News2 days ago An Rufe Shagunan Sayar Da Magani Kusan 600 A Plateau News2 days ago ADC Na Neman Raba Gawuna Da Tsarin NDC Kwankwasiyya Bayan Yimasa Tayin Takarar Gwamnan Kano A 2027 News4 weeks ago Wani Matashi Dan Kano Ya Yanke Gaban Sa News4 weeks ago KANO: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2 A Gwarzo News3 weeks ago Falalar Kwana Goma Na Farkon Zul-Hijjah: Shawarwari Daga Manyan Malamai News4 weeks ago Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano News5 days ago Yadda Faɗan Daba Ya Jefa Al’ummar Kawo Cikin Firgici A Kano Trending News5 days ago Yadda Faɗan Daba Ya Jefa Al’ummar Kawo Cikin Firgici A Kano News5 days ago Kano: Fitaccen Ɗan Kasuwar Man Fetur, Audu Manager, Ya Rasu Yana Da Shekaru 68 News5 days ago Matashi Ya Rasa Ransa Yayin Kokarin Nuna Bajinta Ga Budurwarsa