News
Kungiyar Kwadago Ta Kira Zanga-Zanga Kan Yajin Aikin ASUU
Daga kabiru basiru fulatan
Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta umarci kungiyoyi fiye da 50 da ke karkashinta su fita zanga-zanga bisa yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke yi na tsawon wata uku.
Sojoji Sun Sake Ceto Karin Wata ‘Yar Makarantar Chibok Da Aka Sace
Kungiyar ta ce bayanan da ta samu na nuna babu wani cigaba da ake samu a tattaunawar Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin jami’o’i na ASUU da SSANU da kuma NASU, har ma Kwalejojin Ilimi da na Fasaha.
A taron da suka gudanar ranar Alhamis, Shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya ce matakin ya zamo dole duba da shakulatin-bangaro da gwamnati ta yi wa bukatun kungiyoyin manyan makarantun.
Don haka ya ce za su tabbatar gwamnati ta warware matsalolin kungiyoyin tunda tattaunawar gwamnatin da ASUU ba ta samar da mafita ba.
Wabba ya ce za a gudanar da zanga-zangar ce a fadin kasa baki daya da zummar jan hankalin gwamnati kan illar da yajin aikin ke haifarwa Najeriya da bangaren Ilimi nan da sati guda.
Idan ba a manta ba dai kungiyoyin na yajin aikin ne tsawon watanni kan matsalolin biyansu ta tsarin IPPIS, da sauran bukatu da dama
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
